Tinubu Ya Cancanci Yabo Kan Farfaɗo Da Tattalin Arzikin Nijeriya, Cewar Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

 Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan yadda ya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya daga halin ƙangin da yake ciki.



Sarkin ya bayyana cewa ana samun ci gaba a wasu muhimman fannoni na tattalin arzikin ƙasar, ciki har da bunƙasar tattalin arziki, hauhawar farashi, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje da kuma faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ta hanyar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.


A cewarsa, Najeriya ta fara kafa tubalin samun daidaito a tattalin arzikinta, duk da cewa har yanzu akwai manyan ƙalubalen da ya kamata a magance.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org