NDLEA Ta Gargaɗi Mutane Su Guji Karbar Sakon Kaya Bayan Kama Wata Mace Da Ta Ɓoye Miyagun Ƙwayoyi A Cikin Kwandon Man Ja
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gargaɗi ’yan Najeriya da su guji karɓar kaya ko jakunkuna daga wasu mutane domin kai wa wasu, bayan jami’anta sun gano miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye a cikin kwandon man ja da aka shirya aikawa zuwa Saudiyya.
Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, mai taken “Gargaɗi ga Jama’a”, tare da bidiyon da ke nuna jami’an hukumar suna fitar da wasu abubuwa da aka naɗe cikin leda daga kwandon man.
Babafemi ya ce an ba wata mata da za ta yi tafiya zuwa Saudiyya kayan ne domin ta kai wa wani mutum da ke ƙasar, ba tare da ta san ainihin abin da ke cikinsu ba.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Sai dai jami’an NDLEA sun cafke matar a filin jirgin sama, inda suka gano miyagun ƙwayoyin da aka ɓoye a cikin kwandon.
Ya bayyana cewa da a ce hukumomin Saudiyya ne suka gano ƙwayoyin bayan isar matar ƙasar, da ta iya fuskantar hukunci mai tsanani.
“Ba za mu gajiya da maimaita wannan gargaɗi ba: Kada ku taɓa karɓar wani kaya ko jaka daga wurin kowa domin kai wa wani, ko da kuwa kuna da kusanci da shi,” in ji Babafemi.
Ya shawarci matafiya da su fifita tsaron rayuwarsu da ’yancinsu maimakon tsoron ɓata wa abokai, ’yan uwa ko waɗanda suka sani rai idan suka ƙi karɓar kayan da aka ba su domin kai wa wasu.
Ya ƙara da cewa ya fi kyau mutum ya ɓata wa wanda ya ba shi kaya rai da ya amince ya kai kayan da ba su san abin da ke cikinsu ba, har ya jefa kansa cikin matsalar shari’a.
Haka kuma, kakakin hukumar ya buƙaci ’yan Najeriya su yaɗa wannan gargaɗi ga abokai da ’yan uwansu domin kare matafiya daga fadawa tarkon masu safarar miyagun ƙwayoyi.
NDLEA ta sha yin gargaɗi cewa masu safarar miyagun ƙwayoyi kan yi amfani da amincewa da zumunci wajen yaudarar mutane, su mayar da su masu jigilar haramtattun kayayyaki ba tare da sun sani ba.
Hukumar ta buƙaci jama’a su tabbatar da abin da ke cikin duk wani kaya da aka ba su kafin su amince su kai shi wani wuri, musamman idan za su ketare iyakokin ƙasashe.
An kirkiri wannan hoton ne da taimakon Fasahar AI.
