Wasu zane na addinin musulunci masu ƙayatarwa da aka nuna a taron baje kolin zabe na Halal Exhibition.
Taron da aka gudanar a jihar Kano an shirya shi domin nuna fasahar zayyanar sunayen Allah.
Taron wanda Halal Gallery hadin gwiwa da ma’aikatar tarihi da al’adu suke gudanarwa na da nufin karfafa gwiwar zayyanar sunayen Allah da kuma zaben da musulunci ya yadda da su.
Za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da taron a jihar Kano da zummar baje kolin zayyanar sunayen Allah da kuma rubece-rubucen addinin musulunci.


