Kungiyar masu hakar ma'adanai ta Najeriya ta bukaci a fadada Kwamitin bincike

 

Kungiyar Ma’aikatan Hako Ma’adinai ta Najeriya (NUMW) ta bukaci a gaggauta faɗaɗa kwamitin bincike mai zaman kansa da aka kafa domin gudanar da bincike kan mutuwar masu aikin haƙar ma’adinai 37 da ke hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) a Jihar Neja.

Kungiyar ta yi wannan kira ne  yayin da take yabawa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, kan kafa kwamitin mutum 10, inda ta  bayyana cewa,  ya kamata a faɗaɗa mambobin kwamitin domin su haɗa da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago, gwamnatin Jihar Neja, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, ƙwararrun likitoci da ƙungiyoyin fararen hula.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Hamza Muhammad, ya sanya wa hannu, kungiyar masu hakon ta ce shigar da waɗannan masu ruwa da tsaki cikin kwamitin ya zama dole domin binciken ya samu amincewar ma’aikata, al’ummomin da lamarin ya shafa da kuma sauran jama’a.

Kungiyar ta kuma ce, abin da ya fi damunta shi ne yadda a halin yanzu kwamitin bai ƙunshi wakilan ƙungiyar ma’aikatan da suka rasa rayukansu suke ƙarƙashinta ba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org