Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Nuna Kin Amincewa Da Dokar Sake Fasalin Haraji

 Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi watsi da kudirin gyaran haraji da majalisar dokokin kasa ke nazari akai a halin yanzu. 

An dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa a zauren majalisar, karkashin jagorancin  Jibril Ismail Falgore.

Shugaban masu rinjaye, Lawan Husseini, ya bayyana damuwarsa cewa kudirin zai yi illa ga tattalin arzikin yankin Arewa da kuma kara wahalhalun rayuwa.

Ya kara da cewa, shirin raba kudin haraji na VAT zai bada fifiko ga jihohi irinsu Legas, inda manyan kamfanoni ke da hedikwatarsu.

Lawal Husseini ya yi gargadin cewa hakan na iya raunana wasu jihohin Arewacin kasar, wanda  zai sa su wahalar biyan albashi da kuma kara fuskantar wahalhalun rayuwa.

 Sauran ‘yan majalisar da suka hada da Honarabul Salisu Mohammed da Honarabul Murtala Kadage, sun goyi bayan kudirin, inda suka bukaci ‘yan majalisar Arewa da su hada kai game da wannan kudiri.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Sanatoci, da wakilai, da masu magana da yawun al'ummar jihar, da su nuna kin amincewa da kudirin dokar.

Daga Khadija Aliyu

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org