An Gano Jirgin Ruwa Mai Shekaru 500 Dauke da Arziki a Hamadar Namibia.
Masana tarihi da jami’an hakar lu’u-lu’u sun tabbatar da gano wani jirgin ruwa mai kusan shekaru 500, mai suna Bom Jesus, a yankin bakin teku na hamadar Namibia, yayin aikin hakar lu’u-lu’u da aka gudanar a shekarar 2008.
Bincike ya nuna cewa jirgin, wanda mallakin ƙasar Portugal ne, ya tashi daga Lisbon a shekarar 1533 a hanyarsa ta zuwa ƙasar Indiya, kafin ya gamu da matsala a tekun Atlantika, lamarin da ya jawo nutsewarsa. Tsawon ƙarnuka, yashi da sauyin yanayin teku suka rufe jirgin, lamarin da ya sa aka gano shi a wani yanki da yanzu ke kama da hamada.
A cikin jirgin, masana sun gano manyan dukiyoyi da kayan tarihi, ciki har da: Fiye da hauren giwa 100, Tagulla kusan guda 2,000 (copper ingots) da ake amfani da su wajen cinikayya a wancan lokaci, Tsabar kuɗi na zinare da azurfa sama da 2,000, mafi yawansu daga Spain da Portugal, Da kuma wasu kayan tarihi kamar makamai, kayan aikin jirgi da na rayuwar yau da kullum.
Rahotannin da Jaridar Taskar Labarai ta tattaro game da jirgin sun nuna cewar darajar tsabar kuɗin zinaren kaɗai da aka gano ta kai kusan dala miliyan 13, lamarin da ya sanya wannan ganowa ta zama ɗaya daga cikin manyan gano-gano na tarihi a duniya.
Masana sun bayyana cewa wannan ganowa na bayar da muhimmin haske kan hanyoyin kasuwanci da jigilar kaya a ƙarni na 16, tare da nuna irin rawar da Afirka ta taka a cinikayyar duniya a zamanin mulkin mallaka.
Haka kuma, jami’an tarihi sun jaddada cewar sunan jirgin Bom Jesus ne, ba “Nom Jesus” ba kamar yadda ake yawan faɗi a wasu rahotanni, tare da bayyana cewa ba a tsirƙaƙe jirgin ne a tsakiyar hamada ba, sai dai a bakin teku da sauyin yanayi ya mai da shi hamada a tsawon lokaci.
Masana sun ce ana ci gaba da nazari da adana kayan da aka gano domin kare su a matsayin gadon tarihi na duniya, tare da amfani da su wajen faɗaɗa ilimin tarihin teku, kasuwanci da hulɗar ƙasashe a ƙarni-ƙarni da suka gabata.

