Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai..
Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai
Tauraro kumafitaccen mai shirya fina-finan HausaAli Huhu, ya bayyana Iran a matsayin misali wajen haskaka Musulinci a matsayin adinin zaman lafiya ta hanyar fina-finai. A
Tauraro kumafitaccen mai shirya fina-finan HausaAli Huhu, ya bayyana Iran a matsayin misali wajen haskaka Musulinci a matsayin adinin zaman lafiya ta hanyar fina-finai.
A wata hira ta musamman da da kamfanin dillancin labarai na Iran Press, Ali Nuhu, wanda shi ne babban Manajan Kamfanin Fina-finai a arewacin Najeriya, ya yaba wa Iran saboda kokarin da ta yi wajen bayyana ainihin Musulunci a matsayin addinin zaman lafiya da hakuri ta hanyar yin fina-finai.
Ya kara da cewa Najeriya da Iran sun kuduri aniyar karfafa dangantaka ta hanyar sinima.
Ali Nuhu ya ce tabbas, Iran da Najeriya duka suna da al’adu mabanbanta. Najeriya tana da al’adu daban-daban daga Arewa da Kudu, Wanda kuma hakan zai bada damar yin hadin gwiwa da wasu kasashe.
Iran tana daya daga cikin irin wadannan kasashe, domin muna raba dabi’un al’adu da yawa, musamman da Arewacin Najeriya.
Dangane da wannan batu, za mu hada kai don samar da wani dandali da zai amfani kasashen biyu, ini shi a gefen bikin fina-finai na Zuma International da aka yi a Abuja.
Ali Nuhu y ace akwai bukatar karin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, Misali, Iran tana da masu shirya fina-finai, mu ma muna yi.
Bayan haka, ina tsammanin hadin gwiwar zata samar da hanyar da za a nuna fina-finan Iran a Najeriya, kuma ana iya nuna fina-finan Najeriya a Iran. Wannan zai taimaka wajen gina dangantaka mai dorewa.
Ya kuam ce tuni kasashen biyu suka fara yin amfani da sinima wajen karfafa dangantaka inda A wannan shekarar, ofishin jakadancin Iran ya taka muhimmiyar rawa a bikin fina-finai na duniya na Zuma. A lokacin ƙungiyar, mun yi tarurruka da su kuma mun ƙirƙiri shirye-shiryen haɗin gwiwa,
waɗanda suka yi nasara sosai. A lokacin da nake magana da ku, an nuna fina-finan Iran sama da hamsin a bikin fina-finai na Zuma International Film Festival a nan Najeriya. Mun riga mun fara, kuma muna fatan ci gaba nan ba da jimawa ba.
