Shahararren mawaki dan asalin jihar Katsina, da aka fi sani da Kosan Waka na kwance ranga-ranga ba lafiya
Rayuwa kenan
A nan gwamnan Kano ne ya ziyarce shi a asibiti, inda a bidiyon mawaƙin ko magana bai iyawa ba, sai dai ya daga ido yana ta kallon Abba Gida-gida
Wani abin birgewa, rahotanni sun bayyana cewa gwamnan na Kano ya dauke nauyin biyan duk wani kuɗi na jinyar mawaƙin
Irin wannan kulawar ba kowa ke samun irinta daga wajen gwaninsa ba, ba kowane gwamna , ke iya ziyarar mawaƙinsa ko wani talakawan da ya wahalta masa ba, amma ku dubi yadda gwamnan Kano ya yi irin wannan abin a yaban, duk da shi dama kamar ya saba bada irin wannan kulawar ga masoyansa komin ƙanƙantarsu
Allah Ya ba shi lafiya, shi kuma Abba Kabir Yusuf Allah Ya saka masa da alkairi
@Katsina Daily news

