Jami’an Tsaron Kamaru Sun Kama Matashi Da Harsasan Bindiga

 Jami’an tsaron Jamhuriyar Kamaru sun kama wani matashi mai suna Moussa Ngoudja, mai shekaru 23, dauke da harsasan bindiga a kusa da iyakar Kamaru da Najeriya.



Rahotanni sun ce an kama Ngoudja ne a kauyen Dougoumslio Slio da ke Fotokol, kusa da yankin Gamboru Ngala. An gano cewa ya boye harsasan nau’in 7.62mm a cikin manyan jarkoki da ya ɗora a kan babur.


Bayan kama shi, an kai matashin zuwa hannun jami’an jandarma da ke Hile Alifa, inda yake ci gaba da kasancewa a tsare domin gudanar da bincike kan lamarin.


Rahotannin sun ce hukumomin tsaro na bincike domin gano inda aka samo harsasan da kuma inda ake shirin kai su. Hukumomin ba su bayyana ƙarin bayani kan sakamakon binciken ba tukuna.


#DanmasaniRadio #Kamaru #Najeriya #GamboruNgala #Fotokol #Tsaro #HarsasanBindiga #Cameroon #Nigeria #HausaNews #BreakingNews

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org