Atiku Ya Yi Kira Da A Guji Rikici A Zaɓen Gwamnan Osun
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’a da su guji rikici yayin zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Atiku ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.
Ya kuma yi kira da a tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaɓen, tare da kare ƙuri’un jama’a da kuma martabar tsarin dimokuraɗiyya a jihar.
Atiku ya jaddada cewa gudanar da zaɓe cikin lumana da bin ƙa’idoji zai taimaka wajen tabbatar da cewa jama’a sun samu damar zaɓar shugabannin da suke so ba tare da tashin hankali ko matsala ba.
#Danmasaniradio#AtikuAbubakar #ADC #Osun #OsunElection #INEC #Zabe #Dimokuradiyya #NigeriaPolitics #HausaNews #NigeriaNews
