Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Kwamitocin Dasa Bishiyoyi Miliyan 11 na Shirin KT1T a Faɗin Jihar Katsina
A ranar Alhamis, 27 ga Agusta, 2026, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., ya ƙaddamar da Kwamitocin Dasa Bishiyoyi Miliyan 11 na Shirin Katsina One-Person-One-Tree (KT1T), a wani muhimmin mataki na ƙarfafa kare muhalli da dakile barazana ga sauyin yanayi a faɗin jihar Katsina.
An gudanar da bikin ƙaddamar da kwamitocin ne a ranar Alhamis a
babban dakin taro dake cikin gidan gwamnati, domin samar da ingantaccen tsarin
da zai tabbatar da aiwatar da shirin a ƙananan hukumomi 34 da mazabu 361 na
fadin jihar.
Shirin na daga cikin manufofin gwamnatin Gwamna Radda na
“Building Your Future (BYF)”, kuma an gina shi ne bisa tsarin shuka bishiya
daya ga duk mutun daya na jihar Katsina. Manufarsa ita ce shuka bishiyoyi
miliyan 11 a fadin jihar don ƙarfafa al’umma wajen dasa itatuwa, kare su da
kuma ɗaukar nauyin kiyaye muhalli.
Tsarin kwamitocin matakai huɗun ya ƙunshi Babban Kwamitin
Gudanarwa, Kwamitocin Sa-ido a kowane Zone, Kwamitocin Kula da Aiwatarwa na
Ƙananan Hukumomi, da Kwamitocin Aiwatarwa na Mazaɓu (Ward).
Ga yadda tsarin kwamitocin kamar haka:
Mai bawa gwamna shawara kan harkokin sauyin yanayi, Professor
Al’amin Muhammad zai kasance shugaban shirin na jiha. Hon Abdullahi Aliyu
Turaji zai kasance shugaban kwamitin shiyyar Katsina yayinda Hon Shafi’u Abdu
Duwan zai kasance shuhaban shirun na shiyyar Daura inda Hon Iyaku Dabai zai
kasance jagoran shirin na Futuna Zone. Hakazalika, kowane shugaban karamar
hukuma zai kasance jagoran shiri a karamar hukumarsa yayinda kowane kansila zai
kasance jagoran shirin a mazabarsa.
Kwamitocin za su jagoranci ayyukan shirin a faɗin Yankunan da
suka fi buƙatar shirye-shiryen ayyukan sauyin yanayi (Climate Intervention
Areas) guda 6,652, tare da haɗin gwiwar shirin CDP domin tabbatar da cewa an
kare itatuwan da aka dasa kuma an kula da su yadda ya kamata.
Gwamna Radda ya jaddada cewa nasarar shirin ba za ta ta’allaka
ne kawai kan yawan itatuwan da aka dasa ba, sai dai kan yawan waɗanda suka
rayu, suka girma kuma suka samar da tasiri mai ɗorewa ga al’umma. Ya kuma yi
kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin matasa da mata,
ƙungiyoyin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su mallaki shirin tare da
bayar da cikakken goyon baya.
Ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen yaƙi da kwararowar
hamada da zaizayar ƙasa, tare da ƙarfafa al’umma ga tsarin sauyin yanayi,
bunƙasa noma, inganta lafiyar jama’a da samar da hanyoyin more rayuwa.
Da yake jawabi a wajen taron, Mai Bai wa Gwamna Shawara na
Musamman kan Sauyin Yanayi, Farfesa Al’amin Muhammad, ya bayyana shirin a
matsayin wata muhimmiyar hanya ta tinkarar ƙalubalen muhalli da ke fuskantar
Jihar Katsina. Ya ce haɗin gwiwar al’umma, sa ido akai-akai da kuma kula da
itatuwan da aka dasa za su kasance muhimman ginshiƙai wajen cimma manufofin
shirin.
Shi ma Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautun Gargajiya,
Hon. Bishir Tanimu, ya yabawa Gwamna Radda bisa sanya al’umma a tsakiyar
manufofin kare muhalli. Ya tabbatar da cewa ƙananan hukumomi 34, hukumomin
gargajiya da sauran tsarin shugabanci na matakin ƙasa za su haɗa kai domin
tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirin da dorewarsa.
Gwamna Radda ya sanar da cewa za a fara aiwatar da shirin dasa
itatuwan KT1T a hukumance a faɗin Jihar Katsina daga ranar 10 ga Satumba, 2026,
yayin da kwamitocin da aka ƙaddamar za su fara shirye-shirye da wayar da kan
jama’a gabanin ranar ƙaddamarwar.
Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin
Katsina, Alh Abdulkadir Mamman Nasir, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokoki,
Hon Dabai, kwamishinoni, shuwagabannin kananan hukumomi, kansiloli da sauran
yan kwamitoci.

