A shirye jihar Kano ta ke ta kafa 'yansandan jiha – Gwamna Abba Gida Gida

 Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jihar ta shirya tsaf domin kafa rundunar 'yansandan jiha idan aka samar da tanadin doka da kundin tsarin mulki.



Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da Kwamitin haɗin gwiwar hukumomi kan yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi a gidan gwamnatin Kano.


Ya ce rundunar 'yan sandan jihar za ta yi aiki ne tare da Rundunar 'yansandan Najeriya, ba wai za ta maye gurbinta ko ta yi gogayya da ita ba. Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen inganta tattara bayanan sirri da gaggauta ɗaukar mataki kan barazanar tsaro.


Yusuf ya ce Kano na da ƙwararrun ma'aikata, cibiyoyi da kuma ƙarfin gudanarwa da za su ba ta damar tafiyar da rundunar 'yan sandan jiha idan aka ba da damar kafa ta.


Haka kuma, ya sake tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa ga duk wani sahihin shiri da zai ƙarfafa tsaron ƙasa, tare da bayyana cewa ƙaddamar da kwamitin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na nuna aniyar gwamnati na magance matsalar ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.


Ya kuma buƙaci mambobin kwamitin su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, ƙwarewa da jajircewa.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org