Tashin Hankali a Kano: Matashi Ya Fado Daga Kan Gada Ya Rasu Nan Take

 Wani mummunan al'amari ya girgiza al'ummar Kano bayan da wani matashi ya rasa ransa sakamakon fadowa daga kan gadar Kofar Gadon Kaya.




Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya hau saman ƙarfen kariyar da aka girke a gefen gadar, amma daga bisani ya fado ƙasa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa nan take.


Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin abin da ya sa ya hau saman gadar ba. Sai dai wasu rahotanni na cewa yana iya kasancewa yana cikin yanayin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da hakan.


Wannan lamari ya sake zama darasi ga matasa kan muhimmancin kaucewa duk wani abu da zai iya jefa rayuwa cikin haɗari, musamman shaye-shayen da ke haddasa asarar rayuka da lalata makoma.


Muna addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya ji ƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Haka kuma Allah Ya bai wa iyalansa da 'yan uwansa haƙurin jure wannan babban rashi. Ameen.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org