'Yansanda sun kama mutane huɗu bisa zargin satar jariri daga hannun mahaifiyarsa


Rundunar ’yan sandan Jihar Abia ta kama wasu mutane huɗu bisa zargin satar wani jariri mai kwanaki huɗu da haihuwa daga hannun mahaifiyarsa, wadda ke fama da lalurar tabin hankali, tare da sayar da jaririn ga wani mutum.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Abia, Maureen Chinaka ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin.

Jami'ar ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin da Gladys Nathaniel, mai shekaru 48, Victor Udochukwu mai shekaru 47, Chijioke Obunwa mai shekaru 59 da Onyeonoro Chinwe mai shekaru 43.

A cewar Chinaka, jami’an sashen yaƙi da manyan laifuka, tare da bangaren maida  martanin gaugawa na hukumar ne suka kama waɗanda ake zargin a ranar 16 ga watannan na Satumba 2026, bayan samun bayanan sirri masu karfi da za a iya daukar mataki a kansu.

Ta ce, binciken farko ya gano cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki wajen satar jaririn mai kwanaki huɗu daga hannun mahaifiyarsa, sannan suka sayar da shi ga wani mutum.

Sanarwar ta ce: “Ana zargin waɗanda ake zargin sun haɗa baki wajen satar jariri mai kwanaki huɗu daga hannun mahaifiyarsa mai matsalar tabin hankali, sannan suka sayar da jaririn ga wani mutum.”

Chinaka ta ce jami’an tsaro sun cafke waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike, inda daga bisani aka ceto jaririn da mahaifiyarsa.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org