Cibiyar kula da cututtuka da kare lafiyar jama'a ta gargadi 'yan Najeriya

 

Cibiyar Kula da Cututtuka da Kare Lafiyar Jama’a ta Najeriya (NCDC) ta fitar da sanarwar gargaɗin akan lafiyar jama’a, biyo bayan sabon rahoto kan ci gaba da barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Cibiyar ta ce akwai bukatar  yin  taka-tsantsan, yayin da hukumar take ƙara ƙarfafa matakan sa ido, shiri da mayar da martani domin dakile duk wata barazana da ka iya tasowa daga barkewar cutar.

Daraktan-Janar na kungiyara ta NCDC, Jide Idris, ne ya sanya hannu kan sanarwar.

Hukumar ta ce ana ci gaba da aiwatar da dukkan matakan shirye-shirye, kuma za a riƙa duba tare da sabunta matakan bisa sauye-sauyen yanayin yaɗuwar cutar da kuma kimanta haɗarin da take iya haifarwa ga lafiyar jama'a.

Hukumar ta ce: “Za a ci gaba da duba waɗannan matakai bisa sauye-sauyen yanayin yaɗuwar cutar da kuma kimar haɗarin lafiyar jama’a.”

A matsayin wani ɓangare na ƙara tsaurara matakan sa ido, cibiyar ta shawarci matafiya da ke shigowa Najeriya daga ƙasashen da ake samun yaɗuwar cutar ta Ebola ko kuma waɗanda ke da alaƙa da yaɗuwar cutar, da su cike Takardar Bayanin Lafiya watau (Health Declaration Form).

Ta karav da cewa, matakin na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa sa ido kan lafiyar jama’a da kuma sauƙaƙa bin diddigin matafiya idan buƙatar hakan ta taso.

Cibiyar ta ce: “A halin yanzu, fasinjojin da suka fito daga sauran ƙasashe ba a tilasta musu cike wannan takarda ba.”

sananan hukumar kula da lafiyar ta  buƙaci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan, musamman game da alamomin da suka yi daidai da na cutar Ebola.


Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org