A ƙaddamar da Tsarin Zaman Lafiya, Tsaro da Ci gaban Arewa maso Yamma na 2026
“Ana iya tura jami’an tsaro inda ake rashin tsaro, amma zaman lafiya sai an gina shi. Ana gina zaman lafiya ne kawai ta hanyar magance dalilan da suka kawo shi”— Gwamna Dikko Radda
Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙaddamar da Tsarin Zaman Lafiya, Tsaro da Ci gaban Arewa maso Yamma na 2026–2030, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA) a New York dake kasan Amurka.
Gwamna Radda ya ƙaddamar da tsarin ne a wani taro mai taken “Jihohi Bakwai, Muradi Ɗaya”, inda ya jaddada buƙatar haɗin gwiwar jihohin Arewa maso Yamma wajen magance matsalolin tsaro da ci gaba.
Tsarin zai mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da zaman lafiya, jawo jarin ƙasa da ƙasa, bunƙasa damar matasa da kuma hanzarta ci gaba mai ɗorewa a jihohin yankin.
Taron ya samu halartar wakilar daga jihohin Kano, Kaduna, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara, hukumar cigaba ta Arewa Maso Yamma, abokan hulda da sauran masu ruwa da tsaki.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
September 22, 2026.


