Ina gyara kura-kuran gwamnatocin baya — Shugaba Tinubu.


Shugaba Bola Ahmad Tunibu na Najeriya  ya ce, gwamnatinsa tana gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi ne, don haka  ya kamata 'yan kasar su  sake zaɓar gwamnatinsa domin ta samu damar kammala abin da ta kira kyakkyawan aiki da ta fara.

Shugaban  ya bayyana haka ne a ranar Juma’a ta bakin Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas a lokacin wata addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Shugaba Tinubu ya ce, zaman lafiya da ci gaba, sannu a hankali suna dawowa cikin ƙasar.

“Saƙona ga ƙasar nan a madadin Shugaban Ƙasa, Shugaban Majalisar Dattawa da kuma dukkan ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, shi ne, kada ’yan ƙasa su yanke ƙauna. Zaman lafiya yana dawowa ƙasar nan. Ci gaba yana dawowa ƙasar nan. Al’amura za su inganta yayin da muke ci gaba da wannan tsarin dimokuraɗiyya".

“Abu mafi muhimmanci shi ne ’yan ƙasa su duba abin da gwamnatin yanzu ta mayar da hankali a kai. Kura-kuran baya—wato tarin kura-kuran da aka yi da kuma damammakin da aka rasa a baya—ana gyara su a wannan gwamnati".

“Kuma ina son in bayyana a sarari cewa, Najeriya tana kan turbar da ta dace; akwai haske a ƙarshe, kuma ’yan Najeriya sun riga sun yi sadaukarwa sosai domin ganin ƙasar nan ta sake zama babbar ƙasa.

“Ya kamata mu ƙara bai wa wannan gwamnati dama domin ta dawo ta kammala aikin alherin da ta fara.” a ta bakin shugaban majalisar wakilan

Manyan jami’an gwamnati sun halarci taron, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin da gwamnonin jihohi da  ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa da  ministoci da Sakataren Gwamnatin Tarayya  George Akume  da manyan hafsoshin rundunonin soji.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org