Aliko Dangote da Kasashen Habasha da Djibouti za su gina bututun iskar man fetur na dala miliyan 660
Hamshakin attajirin nan na Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa, yana taimakawa wajen samar da kuɗin aikin gina sabon bututun jigilar man fetur da aka tace, wanda zai haɗa kasashen Habasha da Djibouti, kan kuɗin da ya kai dala miliyan dari shida da sittin.
A ƙarƙashin yarjejeniyar da Kamfanin Zuba Jari na Habasha mai suna Ethiopian Investment Holdings a turance ya sanar a ranar Alhamis da ta gabata, aikin zai ƙunshi gina bututun mai mai tsawon kilomita 120, wanda zai haɗa tashar jiragen ruwa ta Damerjog da wata cibiyar rarraba kayayyaki da ke Dewele.
Kasar Habasha wadda ba ta da mashigar teku, ta dogara sosai da tashar jiragen ruwa ta kasar Djibouti wajen shigo da kayayyaki, ciki har da man fetur da aka tace.
Ana sa ran bututun zai fara aiki cikin watanni goma sha takwas (18). Aikin zai kuma ƙunshi gina wuraren ajiyar man fetur a ɓangarorin biyu na bututun.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ce aikin “zai rage kuɗaɗen sufuri da jinkirin jigilar kayayyaki,” tare da ƙarfafa tsaron makamashi a yankin da bututun zai ratsa.
Aikin ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar Dangote ke ƙara faɗaɗa harkokin gine-ginen ababen more rayuwa da masana'antu a faɗin Afirka.
Ƙungiyar tana kuma gina bututun taki da tashar samar da wutar lantarki da darajarsu ta kai dala biliyan 4, baya ga wata masana'antar kera kayan masarufi na polypropylene a Habasha.
Ana kuma sa ran Dangote zai aza harsashin gina sabuwar matatar mai a Lamu ta ƙasar Kenya, a mako mai zuwa. Matatar za ta kasance tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana.
