Yan Sanda A Katsina Sun Dakile Yunkurin Yin Garkuwa Da Wasu Mutane Su 7

 Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane, tare da ceto mutane bakwai da wasu da ake zargin yan bindiga ne suka tare, akan titin Kankara zuwa Dutsin-ma, a Karamar Hukumar Kankara ta jihar



Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 9:45 na dare, bayan samun kiran gaugawa a ofishin yan sandan Kankara cewa, wasu da ake zargin yan bindiga ne sun tare wani ɓangare na titin Kankara zuwa Dutsin-Ma, kusa da ƙauyen Unguwar Kanawa-Dantudu.


Rahotanni sun bayyana cewa, yan bindigar sun tare wata mota kirar Volkswagen Golf 3 mai lambar rajista BCH 58 SB, wadda Sani Umar mai shekaru 35 ke tukawa, yana ɗauke da fasinjoji shida daga Jihar Kaduna zuwa Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma.


Bayan samun rahoton, Jami’in Yan Sandan Kankara (DPO) ya jagoranci jami’an rundunar Violent Crime Response Unit (VCRU) cikin gaugawa zuwa wurin da lamarin ya faru.


Jami’an sun bi sawun waɗanda ake zargin yan bindigar ne, inda suka yi artabu da su ta hanyar musayar wuta mai tsanani, lamarin da ya tilasta wa yan bindigar tserewa daga wurin.


A yayin wannan samame, jami’an sun yi nasarar ceto dukkan mutanen bakwai da ke cikin motar, wato direban da fasinjoji shida, ba tare da wani rauni ba.


Wadanda aka ceto din sun hada da:


1. Sani Umar, mai shekaru 35 — Direba


2. Emmanuela Anyaba, mai shekaru 20


3. Regina Felix, mai shekaru 19


4. Peace Joseph, mai shekaru 23


5. Mercy Michael, mai shekaru 19


6. Maryam Salisu, mai shekaru 21


7. Nafisa Yakubu, mai shekaru 18


Bayern ceto mutanen, an kai su zuwa asibiti mafi kusa domin duba lafiyarsu, inda aka tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya kuma daga bisani aka sallame su.


A halin yanzu, an sake haɗa waɗanda aka ceto da iyalansu, yayin da rundunar yan sanda ke cigaba da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargin yan bindigar ne da suka tsere.


#rescue #KidnappedVictims #cetonrai #artabu #NigeriaPoliceForce #kttvnews

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org