Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nuna alhininsa kan kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka

 Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nuna alhininsa kan kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, da wani abokinsa a garin Dutsin-Ma, a daren Litinin, 26 ga Oktoba, 2026. 



Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga iyalan mamatan da al’ummar Musulmi.


Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin malamin da ya yi fice wajen wa’azi, da’awa da koyar da addinin Musulunci. Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da sauran waɗanda wannan lamari ya shafa, tare da yi musu fatan samun haƙurin jure wannan rashi.


Gwamnan ya tabbatar wa al’umma cewa hukumomin tsaro suna gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda ake zargi da aikata kisan da kuma gurfanar da su a gaban kotu. 


Ya buƙaci hukumomin da su ƙara ƙaimi wajen bincike domin tabbatar da an gano waɗanda ke da hannu a lamarin


Haka kuma, Radda ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su ba hukumomin tsaro haɗin kai, tare da guje wa duk wani mataki da zai iya haddasa tashin hankali. 


Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa mamatan, Ya ba su Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansu da al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan rashi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org