A wani hari da aka kai a Riyadh Mutane 12 sun rasa rayukansu, wasu 309 sun jikkata.
Kimanin Mutane 12 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 309 suka jikkata sakamakon wani hari da aka kai a filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.
Wannan shi ne hari na uku da aka ruwaito an kai wa filin jirgin saman cikin mako guda, a cewar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasar ta Saudiyya.
Jaridar Saudi Gazette wadda ake wallafawa da harshen Turanci , ta ruwaito a yau Lahadi cewa, harin ya faru ne a jiya Asabar, 10 ga wannan wata na Oktoba.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai ’yan ƙasar Saudiyya huɗu, ’yan Bangladesh biyu, da mutum ɗaya- daya daga ƙasashen Amurka, Masar, Jordan, Siriya, Falasɗinu da Sudan.
Hukumar ta bayyana cewa an garzaya da dukkan waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawar likitoci. Ta ƙara da cewa wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Haka kuma, hukumar ta ce harin ya lalata wasu muhimman kayayyakin more rayuwa na filin jirgin saman, inda ta bayyana cewa ana ci gaba da tantance girman barnar da aka yi.
An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na ɗan lokaci bayan faruwar lamarin, domin bai wa hukumomi damar tantance barnar, tabbatar da tsaron kayayyakin filin jirgin saman, da kuma kare fasinjoji, ma’aikata da muhimman kayayyakin more rayuwa da ake amfani da su wajen gudanar da zirga-zirgar jiragen sama.
A wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, an ce hukumomin Saudiyya da rundunar haɗin gwiwar sojojin ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta sun zargi ƙungiyar Houthi ta Yemen da kai harin.
Sai dai Reuters ta bayyana cewa ƙungiyar Houthi ba ta ɗauki alhakin harin da aka kai a ranar 10 ga Oktoba ba.
Tun da farko, jaridar Saudi Gazette, bisa bayanan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya, ta ruwaito cewa wasu hare-hare guda biyu da aka kai daban-daban a filin jirgin saman a ranar Alhamis sun yi sanadin mutuwar ’yan ƙasar Saudiyya uku tare da jikkata wasu mutane da dama.
