Hukumar hana sha da fataucin kwayoyi a Najeriya ta sake kama wata tsohuwa mai shekaru 83 da laifin safarar miyagun ƙwayoyi

 

Hukumar yaƙi da sha da hana fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta sake kama wata tsohuwa mai shekaru 83 mai suna Uloma Uchechi Sunday, bisa zargin mallakar miyagun ƙwayoyi,  ƙasa da shekara guda bayan da aka same ta da laifin da ya shafi miyagun ƙwayoyi.

An kama tsohuwar ne ranar Larabar  da ta gabata a gidanta da ke  jihar Abia. rahotannin sun nuna cewa, an ɗaure ƙwayoyin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne a ƙugunta da kuma cikin mayafi.

A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a wannan rana ta  Lahadi, an kama tsohuwar ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa tana gudanar da wata sananniyar maɓoyar masu mu’amala da miyagun ƙwayoyi, inda ake zargin tana ɓoye wasu masu aikata laifuka da ke addabar al’ummar yankin.

Babafemi ya bayyana cewa an fara kama Uloma ne a ranar 17 ga Mayun shekarar 2025, tare da ’yarta mai shekaru 32, Chisom Uchechi, a wannan gida.

Ya ce,  jami’an hukumar sun ƙwato gram 50 na methamphetamine, gram 522 na tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira skunk, gram 260 na ganyen tabar wiwi  da kuma gram 12 na tramadol daga hannunsu.

Sanarwar ta ce dukkansu sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi, kuma kotu ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 200 kowannensu. Sun biya tarar, sannan kotu ta sake su.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya yi zargin cewa, tsohuwar ta koma harkar fataucin miyagun ƙwayoyi bayan an sake ta.

Sanarwar ta ƙara da cewa, duk da hukuncin da aka yanke mata, tsohuwar ta koma harkar safarar miyagun ƙwayoyi ba tare da ɓata lokaci ba, har ma ta faɗaɗa harkokinta ta hanyar buɗe wata maɓoya da ake zargin tana ɓoye miyagun mutane a cikinta.



Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org