WANI DA AKE ZARGI DA KISAN KAI YA MUTU A KOTU A BAYELSA

 Wani mutum mai shekaru 50, Bethlehem Nwanlia, wanda ake zargi da hannu a wani shari’ar kisan kai, ya mutu bayan ya faɗi a harabar Babbar Kotun Jihar Bayelsa da ke Yenagoa ranar Talata.


Nwanlia na fuskantar shari’a tare da wasu mutane biyu kan zargin haɗa baki, satar mutane da kuma kisan mutane uku a garin Kalaba da ke ƙaramar hukumar Yenagoa a shekarar 2022. Lamarin ya faru ne a Kotun mai lamba 11, jim kaɗan bayan an dage yanke hukuncin shari’ar zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2026.


Rahotanni sun ce Nwanlia ya riƙe ƙirjinsa yana korafin ciwo kafin ya faɗi a wurin da ake tsare da waɗanda ake shari’a. Jami’an hukumar gyaran hali, ’yan sanda da lauyoyi sun yi ƙoƙarin taimaka masa, kafin daga bisani aka kai shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa. Daga nan aka kai gawarsa ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Yenagoa.


Jami’in hulɗa da jama’a na bangaren shari’ar Jihar Bayelsa, Enoch Okunobo, ya tabbatar da mutuwar Nwanlia. Rahotanni sun ce ya taɓa fama da wasu matsalolin lafiya yayin da yake tsare, amma har yanzu ba a bayyana a hukumance ainihin abin da ya haddasa mutuwarsa ba. Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Musa Mohammed, ya ce bai samu labarin lamarin ba lokacin da aka tuntube shi, amma zai bincika.


#Bayelsa #Yenagoa #KisanKai #KotunBayelsa #Nigeria #Nijeriya #HikayaTV #Labarai

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org