APC a Jihar Katsina Ta Garzaya Kotu Don Neman Soke Takarar Wasu ’Yan Siyasa a Zabe Mai Zuwa.

 


Mu’azu Hassan@ Katsina Times

Majiyoyi daban-daban sun tabbatar wa jaridar Katsina Times cewa jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Katsina, domin neman a soke takarar wasu ’yan siyasa a zaɓe mai zuwa, bisa dogaro da wani sashe na dokar zaɓe ta ƙasa da kuma wani hukuncin Kotun Ƙoli.


Majiyoyinmu sun ce waɗanda ƙarar ta shafa sun haɗa da:

Sani Lawal na jam’iyyar ADC, mai neman kujerar ɗan Majalisar Tarayya daga mazabar Baure da Zango.


Ahmed Yusuf Ibrahim Doro na jam’iyyar ADC, mai neman kujerar ɗan Majalisar Tarayya daga ƙananan hukumomin Mani da Bindawa.


Bello Idris Bakori na jam’iyyar APM, mai neman kujerar ɗan Majalisar Tarayya daga ƙananan hukumomin Bakori da Danja.


Shehu Dalhatu Tafoki na jam’iyyar PDP, ɗan takarar Majalisar Tarayya daga ƙananan hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa.


Isma’il Usman Yandaki na jam’iyyar PDP, mai neman kujerar Majalisar Tarayya daga ƙananan hukumomin Kaita da Jibia.

Jamilu Sani Kayauki na jam’iyyar PDP, mai neman kujerar Majalisar Tarayya daga ƙananan hukumomin Batagarawa, Rimi da Charanci.


Abdurrahman Guga na jam’iyyar PDP, mai neman kujerar Majalisar Tarayya daga ƙananan hukumomin Bakori da Danja.


Sirajo Umar na jam’iyyar ADC, mai neman kujerar ɗan Majalisar Dokokin Jihar Katsina daga ƙaramar hukumar Safana.


Sauran waɗanda ƙarar ta shafa sun haɗa da Aminu Sade daga ƙananan hukumomin Zango da Baure, da Abdulkadir Auwalu, mai neman kujerar ɗan Majalisar Dokokin Jihar Katsina daga ƙaramar hukumar Zango. Haka kuma, akwai Dauda Umar Dauda da Sani Lawal.


Majiyoyinmu sun ce za a ji cikakkun hujjojin da jam’iyyar APC ta Jihar Katsina ta gabatar wa kotu a ranar da za a fara sauraron shari’ar, wadda aka shirya gudanarwa a wani lokaci a ƙarshen wannan watan na Nuwamba.


Majiyoyinmu sun tabbatar mana cewa buƙatar jam’iyyar APC ita ce kotu ta soke takarar waɗannan mutane a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.


I 


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org