Tinubu Ya Taya Ɗansa Seyi Murnar Sarautar Dan Zaki Gwandu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya ɗansa, Seyi Tinubu, murnar naɗa shi sarautar gargajiya ta Dan Zaki Gwandu da Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya yi masa a Jihar Kebbi.
An gudanar da bikin naɗin sarautar ne a ranar Laraba a fadar Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya gode wa Sarkin Gwandu da majalisar masarautar bisa wannan karamci.
Shugaban ya bayyana cewa sarautar, wadda ke nufin Ɗan Zaki na Gwandu, na ɗauke da nauyin jagoranci, jarumtaka da hidimar al'umma, ba wai karramawa kawai ba.
Ya kuma yaba da gudummawar da Seyi Tinubu ke bayarwa wajen tallafa wa matasa da bunƙasa al'umma, musamman ta hanyar ƙungiyar City Boy Movement da sauran shirye-shiryensa.
Tinubu ya buƙaci ɗansa da ya kasance mai tawali'u, tare da amfani da sarautar wajen ƙara jajircewa kan ci gaban matasa, zaman lafiya da hidimar ƙasa.
A ƙarshe, ya yi masa fatan samun hikima da ƙarfin guiwa wajen sauke nauyin da ke tattare da sabuwar sarautar.
