Mutane Biyu Sun Jikkata a Saudiyya Bayan Kakkabo Makamai Masu Linzami

 Hukumar tsaron farar hula ta Saudiyya ta ce mutane biyu sun jikkata, yayin da gine-ginen gidaje uku da motoci bakwai suka lalace sakamakon tarkacen makamai masu linzami guda biyu da aka kakkabo.




Hukumar ta ce tarkacen makaman ya faɗo ne a garuruwan Khamis Mushait da Ahad Rufaidah, bayan mayakan Houthi sun harba makaman masu linzami zuwa Saudiyya.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org