A Afirka ta Kudu An gano gawar mace ta 11 yayin da kashe-kashen mata ke ƙara tayar da hankula

An gano gawar wata mace a wata karamar hukuma da ke gabashin birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa adadin matan da aka gano gawarwakinsu a yankin cikin makonni 10 da suka gabata ya kai  sha daya 11.

Wannan sabon al’amari ya ƙara jawo damuwa kan jerin kashe-kashen mata a ƙasar da tuni ke fama da matsalar tashin hankalin da ake yi wa mata.

‘Yan sanda sun ce an gano gawar matar ne a wani fili a Ekurhuleni a wannan rana ta  Lahadi. Wata motar kamfanin tsaro da ke wucewa ta yankin ce ta hango gawar sannan ta sanar da hukumomi.

A halin yanzu ba a gano sunan matar  da shekarunta ko ainihin abin da ya haddasa mutuwarta ba.

Wannan gano gawar ya zo ne kwana guda bayan da ‘yan sanda suka isa wani wurin da aka gano gawar wata mace a kusa da makabarta, a cikin wannan ƙaramar hukuma.

Shugaban ‘yan sandan lardin, Tommy Mthombeni  ya ce, alamun da aka gani sun nuna cewa an kashe matar ne da duwatsu. Ana sa ran gudanar da binciken gawar domin tabbatar da ainihin dalilin mutuwarta.

‘Yan sanda sun ce sun kama wani mutum da ake zargi yana da alaƙa da wannan kisan,  kilomita 400 daga wurin da aka aikata laifin, bayan da ya bar yankin. Kama mutumin ya sa adadin waɗanda ke tsare bisa zargin alaƙa da jerin waɗannan kashe-kashen ya kai mutum huɗu.

Sai dai hukumomi sun jaddada cewa, har yanzu ba a tabbatar da cewa waɗannan kashe-kashen suna da alaƙa da juna ba.

Duk da haka, lamarin ya ƙara daukar hankalin jama’a, musamman ganin cewa an gano gawarwaki takwas daga cikin 11 a cikin wannan watan kaɗai.

Yawancin sauran wadanda abin ya shafa mata ne masu shekaru tsakanin 20 zuwa 30.



Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org