A kalla mutane 43 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da aka alakanta da siyasa a Afrika ta Kudu

 Akalla mutane 43 ne sukan rasa rayukansu a Afirka ta Kudu cikin watanni tara na farkon wannan shekara, a wasu  hare-haren da ake zargin suna da alaka  da siyasa, yayin da ya rage wata guda kafin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, kamar yadda wani sabon rahoto ya bayyana ranar Juma’a da ta gabata.

Kasar ta Afirka ta Kudu za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 4 ga Nuwamba mai zuwa, yayin da jam’iyyun siyasa ke fatan cin gajiyar rashin jin daɗin da wasu ’yan ƙasa ke nunawa game da jam’iyyar ANC mai mulki, wadda ta kasance ita ce babbar jam’iyyar ƙasar tun bayan ganin karshen mulkin wariyar launin fata  a shekarar 1994.

Rahoton ya ce matsalolin karancin ababen more rayuwa da  aikata laifuka gami da matsalar cin hanci da rashawa na daga cikin abubuwan da suka haifar da wannan rashin gamsuwa

Ƙungiya mai Yaƙi da Laifukan Manyan Ƙungiyoyi Masu aikata Laifin kasa da kasa ta Duniya 'Global Initiative Against Transnational Organized Crime' ta ce, adadin mutanen da aka kashe a hare-haren da ake zargin suna da alaƙa da siyasa a wannan shekara ya riga ya zarce jimillar waɗanda aka kashe a shekarun baya tun lokacin da ƙungiyar ta fara bibiyar irin waɗannan hare-hare a shekarar 2015.

Ƙungiyar mai zaman kanta, wadda ke da hedikwata a Geneva ta bayyana cewa, har yanzu akwai sauran watanni masu haɗari a gaba, yayin da yakin neman madafun ikon siyasa ke ƙara tsananta gabanin zaɓen.

A cewar bayanan da ke cikin rumbun bayanan kungiyar ta  GI-TOC, an samu hare-haren siyasa guda 45 ya zuwa ranar 30 ga Satumba. Yawancin hare-haren da ake kaiwa sun shafi jami’an jam’iyyun siyasa, kansilolin gundumomi, ’yan ƙungiyoyin al’umma da ƙungiyoyin masu  fafutuka, da kuma masu riƙe da sarautun gargajiya.

Haka kjuma, Rahoton ya bayyana cewa, daga cikin mutane 43 da aka kashe, 13 ’yan jam’iyyar ANC  mai mulki ne, yayin da mutane takwas suka kasance daga jam’iyyar MK Party (MKP), wadda tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ke jagoranta.

Yawancin hare-haren sun faru ne a lardin KwaZulu-Natal, wanda ake ɗauka a matsayin sansanin jam'iyyar  MKP. Sai kuma lardin Gauteng, wanda ya ƙunshi birnin Johannesburg, inda aka samu hare-hare 10.

Zaɓen ƙananan hukumomin na bana na zuwa ne a matsayin wani muhimmin gwaji ga goyon bayan ANC, gabanin babban zaɓen ƙasa na shekarar 2029.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org