Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta dakile wani yunkurin harin 'yan bindiga a garin Tsabre
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta dakile wani yunkurin kai harin ’yan bindiga a garin Tsabre da ke ƙaramar hukumar Isa, tare da kwato makaman harba roka guda biyu da wasu kayayyaki da maharan suka bari yayin da suke tserewa.
Wannan lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren jiya Juma’a, a lokacin da wasu ’yan bindiga dauke da makamai suka mamaye garin tare da fara harbe-harbenn kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haddasa firgici tsakanin mazauna yankin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar ta Sokoto Ahmad Rufa’i ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar ta Juma’a.
Ahmad Rufa'i ya ce, bayan samun kiran neman agaji, jami’in ’yan sandan da ke kula da yankin Isa, ya gaggauta tattara jami’an rundunar, ciki har da jami’an Sashen Yaƙi da Satar Mutane da kuma Sashen Tunkarar Manyan Laifuka, domin fuskantar maharan.
A cewarsa, jami’an ’yan sandan sun yi musayar wuta da ’yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu komawa cikin wani daji da ke kusa.
Kakakin ya ce musayar wutar ta yi tsanani kuma ta ɗauki wani lokaci, amma saboda ƙarfin makamai da kuma dabarun da jami’an suka yi amfani da su, sun samu nasarar rinjayar maharan tare da tilasta musu tserewa zuwa cikin dajin, inda wasu daga cikinsu suka samu raunuka ko ma suka rasa rayukansu.
Bayan haka, jami’an rundunar sun gudanar da bincike a cikin dazuzzukan da ke kewaye da yankin inda suka gano makaman harba roka guda biyu da kuma bindiga kirar AK-47 guda biyu marasa harsasai.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun haɗa da wayar Techno mai maballan lamba ba tare da batir ba, tocila, hular sojoji ta daji, hular sanyi, takalman silifa guda biyar da kuma rigar kariya daga ruwan sama.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sokoto, Hayatu Shaffa, ya yaba wa jami’an bisa gaggawar da suka yi wajen tunkarar harin da kuma jarumtakarsu a yayin aiki.Sai kwamishinan ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
