Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa a Gaza Ciki Har da Mata Hudu

 


Akalla Falasɗinawa biyar ne suka rasu ciki har da mata guda hudu, sakamakon wani harin sama da kasar Isra’ila ta kai kan wani ginin gidaje a birnin Gaza da sanyin safiyar yau Asabar, kamar yadda jami’an lafiya da na hukumar kare fararen hula suka bayyana.

Ma’aikatan lafiya sun ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai wata Kirista da ’yarta.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Isra’ila ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba. Harin ya ruguza ginin tare da haddasa gobara.

Wani ganau mai suna Ahmed Al-Dahdouh ya ce: “Muna barci sai kwatsam muka ji hare-hare babu kakkautawa da kuma fashe-fashe. Yara suka farka cikin firgici, suka fara gudu suna ihu.”

Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: “Mun fito da gudu, muka tarar an kai hari kan gidan makwabtanmu, akwai gawawwakin shahidai da suka tarwatse, mata, maza da yara. Sai muka fara fitar da su daga cikin baraguzan ginin, domin gawawwakin sun warwatse a ƙarƙashin tarkacen.”

Tsagaita wutar da Amurka ta shiga tsakani wajen samarwa a Gaza a bara ta tanadi cewa daga bisani za a sake gina yankin. Sai dai an samu ɗan ƙaramin ci gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin, wadda ta kunshi sharuddan Hamas ta kwance makamanta, sannan Isra’ila ta janye dakarunta daga Gaza.

Dahdouh ya ce: “Mu Musulmai ne, kuma waɗannan ’yan’uwanmu Kiristoci ne. Ba su da hannu cikin komai, mutane ne masu zaman lafiya, kuma kowa yana son su. Yanzu mun fitar da gawawwakin su, uwa da ’yarta.”

Isra’ila, wadda ke zargin Hamas da sake tara makamai tare da kai hare-hare da suka saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta, ta ƙara tsananta hare-haren da take kai wa ƙungiyar a cikin ’yan makonnin nan.

Hamas ta musanta ƙoƙarin kai hare-hare ko sake gina makamanta, tana kuma zargin Isra’ila da saba yarjejeniyar zaman lafiya ta Gaza.

Jami’an lafiya a Gaza sun ce akalla Falasɗinawa 1,400 ne aka kashe sakamakon harbin Isra’ila tun bayan tsagaita wutar da aka yi a watan Oktoban bara.


Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org