'Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Gidansa da ke Dutsin-Ma

 Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke garin Dutsin-Ma, Jihar Katsina.


Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ƙofar gidan malamin, inda maharan suka buɗe masa wuta tare da wani aminin nasa.


An garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.


Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu ƙarin bayani kan waɗanda suka aikata kisan ko kuma dalilin kai harin.


Lamarin ya ƙara jefa al’ummar yankin cikin alhini, musamman mabiyan malamin da waɗanda suka san shi.

Katsina Past

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org