Gwamnan jihar Katsina ya taya sabbin shugabnnin riko na Online media Chapel na jihar Murna
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umaru Radda, ya taya sabbin shugabannin Kwamitin Riƙo na sabuwar kungiyar Online Media Chapel ta Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa NUJ reshen Jihar Katsina murna .
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammad ya fitar, Gwamnan ya bayyana kafa Online Media Chapel a matsayin muhimmin mataki wajen ƙarfafa ƙwarewa, da’a da haɗin kai tsakanin masu aikin jarida na kafafen a jihar.
Ya ce aikin jarida ta yanar gizo ya zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da jama’a ke samun bayanai a wannan zamani, lamarin da ke buƙatar ’yan jarida su mayar da hankali kan sahihancin bayanai da ɗaukar alhakin abubuwan da suke wallafawa.
Gwamnan ya buƙaci masu aikin jarida a kafafen intanet su tabbatar da sahihancin bayanai tare da tantance su kafin wallafawa, musamman saboda saurin yaɗuwar bayanai a kafafen sada zumunta.
Gwamnan ya ƙara da cewa, fasahar zamani ta samar da damammaki ga ’yan jarida, amma a lokaci guda ta ƙara musu nauyin tabbatar da cewa, bayanan da suke yaɗawa sahihai ne da kuma daidaito sannan ba sa nuna son kai.
Gwamna Radda ya yi fatan cewa sabuwar kungiyar ta Online Media Chapel za ta zama kafar haɗin kai, bunƙasa ƙwarewar aiki da inganta bin ƙa’idojin da’ar aikin jarida tsakanin mambobinta.
Haka kuma, ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen inganta tattaunawar jama’a cikin lumana, zaman lafiya da ci gaban Jihar Katsina.
A karshe, gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa, shugaban rikon da sauran mambobin kwamitin za su yi aiki tare da ’yan jarida domin ƙarfafa haɗin kai da gina ingantacciyar kungiyar Online Media Chapel a jihar.
An dai zabi Alhaji Shafi'i Alolo na Media Crew a matsayin shugaba, Mustapha Saddiq na Katsina Post Sakataren kwamitin da kuma Zaharaddeen Ishaq na Katsina Times wanda aka naɗa Ma’aji.



