Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya a yammacin Kasar Libya

 

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa a wasu garuruwa da dama a yammacin Libya, lamarin da ya katse wutar lantarki da ruwan famfo, tare da jefa wasu mazauna yankin cikin mawuyacin hali.

Ambaliyar ta faru ne cikin daren jiya  Juma’a, inda kwararar ruwa da laka suka mamaye wasu yankuna tare da tare mutane a cikin motoci da gidaje.


Firaministan Libya, Abdulhamid Dbeibah, ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta tattara tare da tura kayan agaji da sauran aubuwan bukata zuwa wuraren da ambaliyar ta shafa domin tabbatar da daukar matakin gaggawa.


Hotuna da bidiyoyi da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna wasu mutane a makale cikin motoci, yayin da wasu ke kokarin tserewa daga kwararar laka da ruwa.


A garin Mizda wanda ke dauke da mutane 30,000 kuma yake a yankin da ke kusa da hamada a kudancin Tripoli, ambaliyar ta haddasa katsewar wutar lantarki a sassa da dama bayan da Turakun wutar lantarki da dama suka fadi.


Mai magana da yawun karamar hukumar Mizda, Omar Kachaka, ya bayyana cewa ruwan saman ya kuma haddasa barnar dukiya da zaftarewar kasa.


A yankin Bani Walid mai tazarar kusan kilomita 170 daga kudancin Tripoli, jami’an ceto sun gudanar da ayyuka domin kubutar da mutanen da ambaliyar laka ta kwashe da motocinsu.


Haka kuma, magajin garin  Nasmah  Ahmed al-Sid, ya ayyana garin a matsayin yankin da bala’i ya afku, sakamakon dimbin barnar da ruwan sama da kuma ambaliyar  suka haddasa.


Firaministan Dbeibah ya ce yana ci gaba da sanya ido sosai kan halin da ake ciki, inda ya umarci hukumomin da su gaggauta bude hanyoyin da ambaliyar ta rufe tare da dawo da   wutar lantarki , ruwan sha da hanyoyin sadarwa.


Hukumomin ceto da na kananan hukumomi na ci gaba da kokarin taimaka wa mazauna yankunan da ambaliyar ta shafa tare da tantance girman barnar da ambaliyar ta haifar.


Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org