Baƙauye Zai Mayar da Ku Ƙauyawa?” — Ibrahim Masari Ya Kalubalanci Wasu Mutanen Kano

 Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabiru Masari, ya yi tambayoyi kan yadda wasu mutane a Kano ke kallon jam’iyyar APC da kuma rawar da ta taka a siyasarsu.

‎



‎Masari ya yi waɗannan kalamai ne yayin ganawarsa da ƙungiyar Triple R, inda ya ce bai kamata mutanen Kano su bari a raina su ba, la'akari da mutuncinsu, iliminsu da gogewarsu.

‎

‎Ya ce: “Yaushe, da mutuncinku, da iliminku da gogewarku, mutanen Kano, baƙauye zai zo ya mayar da ku ƙauyawa?”

‎

‎Ya kuma tambayi dalilin da ya sa wasu ke danganta duk wata matsala da APC, duk da abubuwan da suka samu a jam’iyyar.

‎

‎A yayin taron, Masari ya bai wa ƙungiyar Triple R naira miliyan 300 domin tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.


Kamawa me za ku ce?


#DC Hausa





Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org