HISBAH TA HARAMTA WA ’YAN MATA TALLA BAYAN ƘARFE 10 NA DARE A KATSINA

 Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta sanar da haramta wa ’yan mata gudanar da sana’ar talla bayan ƙarfe 10 na dare a faɗin jihar. Kwamandan Janar na hukumar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar ranar Talata.



Sheikh Saifullahi ya ce matakin ya biyo bayan rahotannin da hukumar ta samu kan yadda wasu ’yan mata masu talla da dare ke fuskantar barazanar cin zarafi, ciki har da fyade, da kuma shiga wasu ayyukan da suka saɓa wa koyarwar addinin Musulunci. Ya bayyana cewa dokar za ta shafi kasuwanni, tashoshin mota da sauran wuraren da ake gudanar da tallace-tallace a faɗin jihar. Haka kuma, hukumar za ta tura jami’anta muhimman wurare domin sa ido da tabbatar da bin umarnin.


Kwamandan ya kuma gargaɗi iyaye da su kula da ’ya’yansu, musamman ’yan mata, tare da guje wa barinsu suna talla a lokutan dare. A wani ɓangare na jawabin, ya sanar da cewa Hisbah za ta ƙara sa ido kan masu sayar da magungunan gargajiya, musamman waɗanda ke amfani da kalaman batsa wajen tallata hajarsu. Ya kuma yi gargaɗi ga masu gudanar da gidajen karuwai da su rufe su, tare da jaddada cewa haramcin sayar da giya a jihar yana nan daram.


Hukumar ta ce za ta gudanar da ayyukanta bisa tanade-tanaden dokar da ta kafa ta, tana mai cewa manufarta ita ce gyara da tabbatar da bin ƙa’idojin da suka dace, ba gallaza wa jama’a ba.


Shin kuna ganin wannan mataki na Hisbah zai taimaka wajen kare lafiyar ’yan mata masu talla, ko kuwa ya kamata a samar musu da wasu hanyoyin samun abin dogaro da kai?

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org