A baya Nafiu Bala sai ya roki kuɗin mota amma yanzu motocin alfarma yake hawa - Inji Nwosu tsohon shugaban ADC

 Wanda ya kafa jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, Nafiu Bala, ya koma amfani da motocin alfarma masu sulke, bayan a baya yana neman taimakon N50,000 na kuɗin mota domin halartar tarukan jam’iyyar.




Nwosu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan rediyon Lagos Talks ranar Laraba, inda ya ce salon rayuwar Bala ya sauya bayan shigar da ƙara kan rikicin shugabancin jam’iyyar a watan Satumban 2025.


Ya yi zargin cewa Bala ya koma zama a manyan otal-otal, tare da rakiyar jami’an tsaro da amfani da sama da motoci uku masu sulke.


Nwosu ya ce a baya idan ya gayyaci Bala taro a Abuja, sai ya aika masa da N50,000 domin ya samu kuɗin motar bas zuwa wurin taron.


Haka kuma, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da hannu a rikicin cikin gida na ADC, yana mai cewa akwai faifan bidiyo da ke nuna shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa yana ƙarfafa wasu mutane su zauna a jam’iyyar domin lalata ta.


Sai dai babu martanin Nafiu Bala ko gwamnatin tarayya kan waɗannan zarge-zargen a cikin rahoton.


Zargin na zuwa ne a daidai lokacin da ADC ke fama da rikicin shugabanci tsakanin ɓangaren David Mark da na Nafiu Bala.


A ranar 5 ga Nuwamban 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark, tare da rusa matakan da ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org