Kotu ta ɗaure Faisal Maina shekaru bakwai a gidan yari

 Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tura Faisal Maina, ɗan tsohon shugaban hukumar gyaran fansho, Abdulrasheed Maina, gidan gyaran hali domin ya fara zaman hukuncin ɗaurin shekara bakwai.


Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da umarnin bayan hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta shigar da buƙatar gaggawa a gabansa.


An sake kama Faisal ne a ranar 14 ga Oktoba, 2026, bayan jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun miƙa shi ga EFCC, sakamakon gujewa beli da kuma kin halartar shari’arsa tun kimanin shekaru shida da suka gabata.


A shekarar 2019 ne aka gurfanar da shi a gaban kotun bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi safarar kuɗaɗen haram da kuma rashin bayyana cikakkun bayanai a takardar bayyana kadarorinsa.


Sai dai bayan an ba shi beli, Faisal ya tsere, lamarin da ya sa kotun ta ci gaba da shari’ar ba tare da shi ba.


A ranar 7 ga Oktoba, 2021, Mai shari’a Okon Abang ya same shi da laifi, inda ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a tuhume-tuhume na ɗaya da na uku, da kuma shekaru 14 a tuhuma ta biyu.


Daga bisani, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauya hukuncin a ranar 24 ga Nuwamba, 2022, inda ta tabbatar da ɗaurin shekaru uku a tuhuma ta ɗaya, bakwai a ta biyu da shekaru uku a ta uku, dukkansu za su gudana a lokaci guda.


A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Omotosho ya umarci cewa a fara ƙirga wa’adin zaman gidan yarin daga ranar 14 ga Oktoba, 2026, wato ranar da aka sake kama Faisal.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org