Fiye Da Malaman Addinin Musulunci 1,000 Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Neman Tazarce

 

Fiye da malaman addinin Musulunci 1,000 ne suka bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya sake neman zaɓe a karo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, suna nuni da matsalar tattalin arziki, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.


An bayyana wannan matsaya ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ƙarshen wani taron ƙasa mai taken “Tantance Halin da Ƙasa Ke Ciki a Mulkin Shugaba Tinubu da Zaɓen 2027”, wanda aka gudanar a Jihar Kano ranar Lahadi.


Sanarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) da kuma Ƙadiriyya, tare da wasu ƙungiyoyin Musulunci, suka nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a zaɓen 2027, tare da kira ga mambobinsu a faɗin ƙasar da su goyi bayan sake zaɓensu.


JIBWIS da Ƙadiriyya sun bayyana goyon bayansu ga takarar Tinubu ne a yayin ziyarar da Sanata Abdul’aziz Yari, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, ya kai wa shugabannin ƙungiyoyin.


Sai dai malaman addinin da suka haɗa kansu ƙarƙashin Ko Da Naka… For the Struggle to Promote Good Governance and Community Development, tare da haɗin gwiwar AFAQ Educational Foundation, sun bayyana rashin gamsuwarsu da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke tafiyar da ƙasar.


Malaman sun cimma matsaya baki ɗaya cewa manufofin tattalin arzikin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin canjin kuɗin Naira, ƙarin kuɗin wutar lantarki da sauye-sauyen haraji, sun ƙara wa talakawa nauyin rayuwa.

Taron ya bayyana rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da gwamnatin Tinubu, musamman ci gaba da aiwatar da manufofin tattalin arzikin da mahalarta suka ce sun ƙara tsananta wahalhalun da talakawa ke fuskanta.


Sanarwar ta ce: “Abin takaici ne yadda gwamnati ta ci gaba da dagewa wajen aiwatar da waɗannan manufofi, waɗanda ke ƙara tsananta wahalhalu ga al’umma, maimakon ta sake duba su tare da gyara su. Gwamnati ta fifita ƙara yawan kuɗaɗen shigarta a daidai lokacin da tsadar rayuwa da rashin aikin yi ke barazana ga rayuka da jin daɗin ’yan ƙasa.”


Sanarwar ta ƙara da cewa: “Saboda haka, mahalarta taron sun amince baki ɗaya cewa bai dace a sake zaɓar wannan gwamnati a zaɓen gama-gari na 2027 ba, idan ba ta sauya manufofinta na tattalin arzikin da ke haifar da wahala ba.”


Haka kuma, mahalarta taron sun nuna damuwa kan ci gaba da kashe-kashe da garkuwa da mutane da ’yan bindiga ke yi, da sauran ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar.


Saboda haka, sun yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar.


Sanarwar ta ce: “A madadin haka, ya kamata Shugaban Ƙasa ya janye daga neman takara a zaɓen 2027. Idan ya ƙi yin hakan, ya zama wajibi ’yan ƙasa su ƙi amincewa da takararsa, su kuma bai wa waɗanda suke ganin za su iya samar da ingantaccen shugabanci damar jagoranci.”


Wasu daga cikin malaman da suka gabatar da jawabai a taron sun haɗa da Dr Abdulmuɗɗalib Ahmad Giɗaɗo, Farfesa Muhd Muslim Ibrahim, Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid, Dr Aminu Isma’il Sagagi, Dr Najibullah Abdallah Nuhu, Sheikh Abdurrazaq Uba Musa, Sheikh Musa Muhd Ɗan Kwano, Barrister El-Zubair, Dr Yahuza Getso, Farfesa Ibrahim Siraj Adhama, Dr Umar Dokaji da Sheikh Muhd Sani Khamis (Abu Haisam).

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org