Amnesty International Ta Yi Allah-Wadai Kan hana Taron nuna ci gaba da mulkin Tinubu


Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International reshen Najeriya, ta yi Allah-wadai da zargin hana gudanar da wani taron na kyamar ci gaba bdavmulkin Tinubu mai ntakenn  ‘Tinubu-Must-Go’ a Jihar Kano, inda kungiyar ta zargi ’yan sanda da take haƙƙin ’yan ƙasa na yin tarayya da gudanar da taruka cikin lumana.



Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a jiya Lahadi, inda ta ce, jami’an ’yan sanda dauke da manyan makamai sun toshe  hanyar da ta nufi wurin da aka shirya gudanar da taron.

Amnesty ta bayyana matakin a matsayin hana harkokin siyasa na lumana ba bisa ƙa’ida ba, tare da kira ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ta daina abin da kungiyar ta kira take haƙƙin ɗan Adam cikin rashin kulawa.

“Dole ne ’Yan Sandan Najeriya su daina irin wannan take haƙƙin ɗan Adam cikin rashin kulawa. Magoya bayan dukkan ’yan takara da jam’iyyun siyasa suna da cikakken haƙƙin gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.” inji Kungiyar.

Ta jaddada cewa ’yan sanda suna da alhakin taimakawa wajen tabbatar da gudanar da tarukan siyasa cikin lumana, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ko ɗan takarar da ake goyon baya ko adawa da shi ba.

Amnesty ta ƙara da cewa, “Aikin ’yan sanda shi ne tabbatar da cewa ana gudanar da irin waɗannan tarukan siyasa cikin lumana, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ko ɗan takarar da ake goyon baya ko adawa da shi ba.”

Haka kuma, Amnesty  ta bayyana abin da ya faru a Kano a matsayin wani ɓangare na abin da ta ce, wata alama ce mai tayar da hankali ta takura wa ’yan adawa da jami’an tsaro ke yi a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar Amnesty, hare-hare da barazana da ake ci gaba da yi wa magoya bayan ’yan adawa na iya kawo cikas ga ’yancinsu na yin tarayya da juna da kuma shirya tarukan jama’a cikin lumana.




Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org