Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Masu Bashi Shawara Uku, Ya Buƙace Su da Yin Aiki Bisa Amana

 Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya rantsar da Dr. Surajo Yakubu Batagarawa, Abubakar Kabir Kusada, da Alhaji Ahmed Abduljalal Dandume a matsayin Mashawarta na Musamman ga Gwamnatin shi, tare da zama mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina.





A jawabin shi bayan kammala rantsuwar, Gwamna Radda ya bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin mutanen da suke da ƙwarewa da gogewa, yana mai nuna fatansa na ganin sun yi amfani da iliminsu da basirar su wajen inganta ayyukan gwamnati da samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar jihar.


Gwamnan ya buƙaci sabbin mashawartan da su gudanar da ayyukansu bisa amana, gaskiya da riƙon amana, tare da yin aiki kafada da kafada da sauran mambobin Majalisar Zartarwa wajen cimma manufofin gwamnati.


Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, Sakataren Gwamnati, Barr. Abdullahi Garba Faskari, Shuwagabannin Kananun Hukumomi da sauran yan uwa da abokan arziki.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org