’Yan Sandan Ogun Sun Tsare Jami’ansu Hudu Kan Zargin Cin Zàrafín Wani Matashi

 Hukumar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta tsare jami’anta huɗu bisa zargin cin zarafin wani matashi a yankin Ijagba, Sango-Ota, bayan wani bidiyo da ya nuna yadda jami’an ke riƙe da shi tare da ɗaure masa ankwa ya yaɗu a kafafen sada zumunta.


Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bode Ojajuni, ne ya bayar da umarnin tsare jami’an a hedikwatar rundunar da ke Eleweran, Abeokuta, yayin da aka fara bincike kan lamarin.


 Kakakin rundunar, Oluseyi Babaseyi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.


Ya ce binciken ya biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna jami’an ’yan sanda tare da wani farar hula suna danne matashin tare da sanya masa ankwa.


A cikin bidiyon, an ji wata murya tana zargin cewa jami’an sun ci zarafin matashin ne saboda sanya wando irin na sojoji.


Babaseyi ya ce kwamishinan ’yan sandan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ɗaukar matakin da ya dace.


Ya ƙara da cewa an fara matakan ladabtarwa kan jami’an da abin ya shafa domin tabbatar da gaskiyar lamarin.


Rundunar ta kuma gode wa al’umma bisa sanar da ita bidiyon, tare da kira ga duk wanda yake da sahihan bayanai game da abin da ya faru da ya taimaka wa masu gudanar da binciken.


Haka kuma, ta buƙaci jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, waɗanda ka iya kawo cikas ga binciken.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org