An Gano Sawun Ƙafafun Mutane da Suka Shude Tsawon Shekaru Masu Dubu 23,000 a Amurka.
Masana kimiyya sun gano wasu tsoffin sawun ƙafafun mutane a wurin shakatawa na White Sands National Park, da ke jihar New Mexico a Amurka, waɗanda aka kiyasta shekarunsu ya kai tsakanin 21,000 zuwa 23,000.
An gano sawun ne a bakin wani tsohon tafki, inda aka ce mutane suka taɓa taka ƙasa mai laushi tun a zamanin ƙanƙara. Abin mamaki shi ne, yawancin sawun sun yi kama da na yara da matasa, lamarin da ke ba masana damar hasashen irin zirga-zirgar mutane a yankin a wancan lokaci.
Masana sun yi amfani da binciken sinadarin Carbon-14 wajen tantance shekarun wasu ƙwayoyin tsirran ruwa da aka samu a cikin laka da ke kewaye da sawun.
Wannan bincike ya ƙara ƙalubalantar tsohuwar fahimtar masana tarihi cewa mutanen Clovis, waɗanda suka rayu kimanin shekaru 13,000 da suka wuce, su ne farkon mutanen da suka zauna a Arewacin Amurka.
Binciken ya nuna cewa mutane sun kasance a nahiyar tun dubban shekaru kafin wannan lokacin, har ma a zamanin da ake kira Last Glacial Maximum, lokacin da sanyi ya yi tsanani a sassa da dama na duniya.
Baya ga sawun mutane, an kuma gano na manyan dabbobin zamanin ƙanƙara, ciki har da Mammoth, Ground Sloth da Dire Wolves.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda waɗannan sawun suka iya kasancewa a doron ƙasa na tsawon dubban shekaru ba tare da ɓacewa ba, har suka zama wata muhimmiyar shaida da ke taimaka wa masana kimiyya fahimtar rayuwar mutanen da suka rayu a duniya tun zamanin da.
Mamman Modukur
