Makusantan Gwamna da suka lalata allon tallar Shugaba Tinubu shi ne tushen Matsalar - Ibrahim Masari.

 Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Masari, ya bayyana cewa saɓanin da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya samo asali ne tun bayan da aka buga fastocin tallar neman zaɓen karo na biyu ba tare da saka hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.


Masari ya ce yaran Gwamnan da wasu makusantansa ne suka fara buga fastocin, inda ba a saka hoton Shugaban Ƙasar ba.


Ya ƙara da cewa daga baya shi da Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttaqa Rabe, da Jabiru Tsauri, sun haɗa kuɗi domin buga sabbin fastoci da allunan talla da ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu, Mataimakinsa, Gwamna Radda, tsofaffin gwamnonin jihar biyu, da shi Ibrahim Masari, da Muttaqa Rabe tare da kuma Jabiru Tsauri.


Masari ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya kuma zargi wasu makusantan Gwamnan Katsina, ciki har da Babban Dogarinsa da jami’in ƴan sanda mai kula da harkokin tsaro (CSO), da hannu wajen lalata wasu daga cikin allunan tallar.


Sai dai waɗannan zarge-zarge dai na daga cikin bayanan da Ibrahim Masari ya yi yayin hirar. Mene ne ra'ayoyinku?


– Jaridar Arewa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org