Duk Wanda Ya Samu Matsayi Ko Mukami a Najeriya, Musamman a APC, Rigar Marigayi Buhari Ya Shiga”– Gwamna Radda a Sandamu

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa Marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin siyasa da shugabanci a Najeriya, inda ya ce da yawa daga cikin waɗanda suka samu matsayi ko muƙamai a ƙasar, musamman a jam'iyyar APC, sun amfana da siyasarsa da jajircewarsa.





Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen gangamin yaƙin neman sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Katsina na 2027 a Ƙaramar Hukumar Sandamu.



Ya ƙara da cewa Ƙaramar Hukumar Sandamu na daga cikin ƙananan hukumomin da suka amfana da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin sa ta gudanar, yana mai cewa akwai dalilai da dama da ya kamata al'umma su yi la'akari da su wajen sake ba gwamnatin dama a karo na biyu.



Dangane da takarar Alhaji Yusuf Buhari, ɗan Marigayi Muhammadu Buhari, a kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Daura/Sandamu/Mai'Adua, Gwamna Radda ya bayyana cewa kasancewar ɗan Marigayin a matsayin ɗan takara a yankin, bai kamata ace za'ayi tallar neman zaben shi ba, sai dai al'ada ta siyasa.


Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatin sa ta gudanar da ayyukan raya ƙasa da suka cancanci a sake duba su a zaɓen 2027, yana mai danganta nasarorin da aka samu da damar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa gwamnatocin jihohi, wanda hakan ne zai bada damar sake zaɓen jam'iyyar daga sama har ƙasa.


MS Ingawa

SSA, Media & Strategy 

Katsina State Government 


November 15, 2026. 


#Tinubu2027 #Radda2027 #BuildingYourFuture #KatsinaDecides

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org