Kasar Iran na shirin fara aiki da tsarin fasahar nukiliyanta na farko da ta kera a cikin gida
Kasar Iran na shirin fara aiki da tsarinta na farko na fasahar nukiliya da ta kera a cikin gida, inda aikin ke nuna ci gaban da kasar ta samu a fasahar nukiliya ta zamani, kamar yadda shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) ya bayyana a yau Lahadi.
Da yake jawabi a wata hira da aka watsa a talabijin, Mohammad Eslami ya ce, masana kimiyya na Iran sun samu gagarumin ci gaba wajen samar da tsarin, yana mai bayyana fatan cewa shirin zai fara aiki bisa ga jadawalin da aka tsara.
Ya ce aikin na da nufin nuna iyawar kimiyya ta kasar ta Iran da kuma ikon gogayya da manyan kasashen duniya a fasahohin zamani.
Shugaban kwamitin Fasahohin Zamani na Iran Ali Nowrouzi, ya bayyana cewa fasahar fusion ta nukiliya ta kunshi hada isotopes guda biyu masu sauki a karkashin wasu yanayi na musamman masu sarkakiya.
Ya ce hasken da ake samu ta wannan tsari za a iya amfani da shi wajen kera magungunan da kuma nagartattun tsare-tsaren binciken likita.
Nowrouzi ya kara da cewa dogon burin shi ne samar da tsarin da zai iya samar da manyan magudanan wutar lantarki ba tare da asarar makamashi a cikin tsarin ba, wanda ke nuna babban damar da fasahar fusion ke da ita wajen samar da makamashi.
