Al'ummar kasar Cape Verde sun fito zaɓen sabon shugaban ƙasa.

Al'ummar ƙasar Cape Verde sun fara kada ƙuri'unsu domin zaɓen sabon shugaban ƙasa, inda ake ganin shugaban mai ci, José Maria Neves, na da babban damar lashe zaɓen domin samun wa'adin mulki na biyu.

Neves na fafatawa da Joana Rosa Amado, tsohuwar Ministar Shari'a, wadda ita ce mace ta farko da ta tsaya takarar shugabancin ƙasar, tare da wasu 'yan takarar jam'iyyun adawa huɗu.

Joana Rosa na samun goyon bayan jam'iyyar adawa ta Movement for Democracy, wadda ta shafe shekaru 10 tana mulkin ƙasar kafin ta sha kaye a zaɓen 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a watan Mayun da ya gabata.

A yayin yakin neman zaɓen, 'yan takarar sun fi mayar da hankali kan samar da ayyukan yi ga matasa da kuma rage yawan 'yan ƙasar da ke yin ƙaura zuwa ƙasashen waje, musamman ganin cewa yawan 'yan Cape Verde da ke zaune a ƙetare ya fi waɗanda ke zaune a cikin ƙasar.

Shugaba Neves ya yi alƙawarin shirya taron matasa na ƙasa idan ya sake samun nasarar lashe wa'adin mulki na biyu. Ita kuwa Joana Rosa ta ce wajibi ne gwamnati ta samar da yanayin da zai bai wa matasa damar gina makomarsu a cikin ƙasarsu, maimakon tilasta musu barin ƙasar domin neman abin yi.

Fiye da mutum 300,000 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a zaɓen, wanda aka tsara rufe rumfunan zaɓe da ƙarfe 6 na yamma agogon ƙasar a ranar Lahadi. Ana sa ran hukumar zaɓen za ta sanar da sakamakon wucin gadi cikin kwanaki biyu zuwa uku.

Haka kuma, kusan masu sa ido kan zaɓe 150 daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Tarayyar Afirka (AU) da Tarayyar Turai (EU) ne ke sa ido kan yadda ake gudanar da zaɓen.

Idan babu ɗan takarar da ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, za a sake gudanar da zaɓe tsakanin 'yan takara biyu da suka fi samun ƙuri'u a ranar 29 ga watan Nuwamba.

Cape Verde ƙasa ce da ke cikin Tekun Atlantika, mai tazarar kusan kilomita 600 daga gabar tekun Senegal. Ƙasar ta ƙunshi tsibirai 10 da suka samo asali daga aman wutar duwatsu, kuma tana ƙara samun karɓuwa a matsayin wurin yawon buɗe ido.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org