Matasa 3 sun mutu yayin kokarin ciro waya daga cikin shadda a Zariya
Wasu matasa uku sun mutu a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata wayar hannu da ta faɗa cikin shadda a yankin Tudun Kusa da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Matasan, Najashi Haruna mai shekara 18, Abdullahi Adamu mai shekara 20 da Ashafa Jumare mai shekara 22, sun mutu ne ɗaya bayan ɗaya a ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce wayar wani mutum mai suna Murtala ce ta faɗa cikin shaddarsa, inda ya yi tayin ba da Naira 1,000 ga duk wanda ya shiga ya ciro masa wayar.
An ce matashi na farko ya shiga da igiya amma igiyar ta tsinke, ya faɗa cikin shaddar. Na biyu ya shiga domin ceto shi, amma shi ma bai fito ba. Daga bisani na uku ya shiga domin ceton abokansa, shi ma ya rasu.
Shugaban ƙauyen Tudun Kusa, Jibrin Suleiman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami'an tsaro sun ziyarci wurin.
#Aminiya.ng
