Tarihin Rayuwar Kwamishinan Ƴansandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage

CP Ali Umar Fage babban jami’in rundunar ’yan sandan Najeriya ne, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana hidimar ƙasa a fannin tabbatar da tsaro, binciken laifuffuka da gudanar da ayyukan rundunar ’yan sanda.



CP Ali Umar Fage ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Fagge ne. Ya yi karatun jami'a a Jami'ar Bayero da ke Kano, inda ya samu digirin farko (Bachelor of Science) a fannin Kimiyyar Siyasa (Political Science).


Ya shiga aikin rundunar ’yan sandan Najeriya ne a ranar 10 ga watan Yuni, 1994, a matsayin Cadet Assistant Superintendent of Police (C/ASP). Tun daga wannan lokaci ya fara gudanar da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, inda ya samu ƙwarewa a fannoni da dama.


A tsawon shekarun aikinsa, ya riƙe muƙamai daban-daban a rundunonin ’yan sanda na jihohin Sokoto, Kaduna, Jigawa, Kano, Katsina da Legas.


A Jihar Sokoto, ya taɓa riƙe muƙaman Officer in Charge (OC) MSS, State Paymaster, OC A-22, da kuma Divisional Police Officer (DPO) na sassan Denge Shuni da Wamako.


A Jihar Kaduna kuma, ya yi aiki a matsayin OC Anti-Vandalisation da DPO na Kurmin Mashi. A Jihar Jigawa kuwa, ya riƙe muƙamin DPO na Ringim.


A Kano, ya taɓa aiki a matsayin Officer in Charge, Monitoring Unit, Zone 1, Kano.


Haka kuma, ya yi ayyuka da dama a Jihar Katsina, inda ya riƙe muƙaman DPO a sassan Kankara, Makera Funtua, Malumfashi, Dutsinma, CPS Funtua, Sabon Garin Daura, Charanchi, Sabon Garin Katsina da Dandume.


Bayan haka, ya riƙe wasu manyan muƙamai a rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, waɗanda suka haɗa da Deputy Area Commander na Metro Area Command, Officer in Charge Monitoring Unit, Second-in-Command na Criminal Investigation Department (CID), Assistant Commissioner of Police (ACP) mai kula da Finance and Administration, da Deputy Commissioner of Police (DCP) mai kula da Finance and Administration a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Legas.


Daga baya an mayar da shi Kwalejin ’Yan Sanda ta Ikeja da ke Jihar Legas, inda ya yi aiki a matsayin Mataimakin Kwamandan Kwalejin (Deputy Commandant), kafin daga bisani a tura shi Jihar Katsina domin jagorantar rundunar ’yan sandan jihar.


A fannin ƙarin ilimi da ƙwarewar aiki, CP Ali Umar Fage ya halarci kwasa-kwasai na musamman da suka haɗa da Advanced Detective Course a Police Staff College da ke Jos, da kuma Strategic Leadership and Command Course. Waɗannan kwasa-kwasai sun ƙara masa ilimi da ƙwarewa a fannin bincike, jagoranci da gudanar da ayyukan tsaro.


A ranar 30 ga watan Maris, 2026, CP Ali Umar Fage ya karɓi ragamar shugabancin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina a matsayin Kwamishinan ’Yan Sanda na 27 a tarihin jihar, bayan an tura shi wannan muƙami bisa umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya.


Bayan karɓar wannan muƙami, ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Katsina, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da aikata laifuffuka.


Ya kuma jaddada amfani da dabarun tsaro na zamani da kuma matakan da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jihar.


CP Ali Umar Fage na daga cikin manyan jami'an ’yan sandan Najeriya da suka samu gogewa ta tsawon shekaru a fannoni daban-daban na aikin tsaro, bincike, gudanarwa da jagoranci.


Tarihinsa ya nuna irin tafiyar da ya yi a cikin rundunar ’yan sandan Najeriya, tun daga shigarsa aiki a shekarar 1994 har zuwa zama Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina a shekarar 2026.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org