Faskari Ta Samu Babban Asibiti a Karo na Farko a Tarihinta
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da babban asibiti na farko a tarihin Ƙaramar Hukumar Faskari, a matsayin cika ɗaya daga cikin alkawuran da ya ɗauka ga al’ummar yankin a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.
![]() |
Asibitin, wanda aka inganta daga Cibiyar Kula da Lafiya(CHC), zai samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar Faskari da mazauna yankunan da ke makwabtaka da ita, tare da kusantar da ayyukan jinya zuwa ga al’umma.
Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, Kwamishinan Lafiya, Hon. Musa Adamu Funtua, ya yaba wa Gwamna Radda bisa ba da muhimmanci ga bunƙasa harkokin kiwon lafiya da kuma cika alkawuran da ya ɗauka ga al’umma.
Ya bayyana cewa wannan mataki zai ƙarfafa tsarin samar da kiwon lafiya, inganta samun muhimman ayyukan jinya, tare da rage buƙatar tafiya mai nisa domin samun kulawar lafiya ta musamman.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Governmen
.png)