Gwamna Radda - "Mun cika alkawurran da muka daukar maku a shekarar 2023"


Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda ya bayyana cewa, Ya cika dukkan alkawurran da ya dauka a yayin neman zabensa a shekarar 2023. yayin gangamin neman sake zabensa a zabe a karamar hukumar Faskari. “mun  Cika Alkawuran da Muka Daukar Muku a 2023, Muna Bukatar Goyon Bayanku a  zaben 2027 Don Dorawa Daga Inda Muka Tsaya”  sai gwamna Radda, ya yi kira ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Faskari da su sake ba da goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shi kansa a zaɓen 2027, domin ci gaba da bunƙasa nasarorin da aka samu da kuma tabbatar da dorewar ayyukan raya ƙasa.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a yayin gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko na 2027 a Faskari, inda dubban magoya bayan Jam’iyyar APC suka taru don sake jaddada goyon bayansu ga jam’iyyar APC da shugabanninta.

Gwamna Radda ya sake bayyana nasarorin da  gwamnatinsa ta samu  a fannoni daban-daban na ci gaba, yana mai cewa cika alkawuran da aka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen da ya gabata, ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen inganta rayuwar al’umma.

Gwamnan ya jaddada buƙatar ƙarin goyon bayan al’umma a zabe mai zuwa na  2027 domin ƙarfafa nasarorin da aka samu da kuma ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Taron ya samu halartar dimbinn magoya bayan jam'iyyar da suka hada da  Shugaban Ƙaramar Hukumar Faskari  Surajo Aliyu Daudawa, wanda ya gabatar da jawabin maraba, tare da jawaban Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha, Dr. Bishir Gambo Saulawa, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Kankara/Faskari/Sabuwa, Hon. Hamza Sule Faskari, da ɗan takarar Sanatan Katsina ta Kudu, Hon. Muntari Dandutse da sauran masu ruwa da tsaki. 


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org